Hukumar Kare hakkin masu siyan kayayyaki ta ƙasa (FCCPC) ta kaddamar da wani shiri a jihar Kano domin dakile hauhawar farashi da hana sayar da kayayyakin jabu ko marasa inganci.
An fara wannan yunkuri a Kasuwar hatsi ta Dawanau, inda hukumar ta gana da ‘yan kasuwa tare da bayyana cewa manufarta ita ce tabbatar da adalci, gaskiya da inganci a kasuwanci, ba tsangwama ba.
Mataimakin shugaban FCCPC, Tunji Bello, ya bayyana damuwa kan masu ɗaga farashi ba tare da hujja ba da kuma masu siyar da kaya marasa inganci.
Shugaban ƙungiyar kasuwar, Alhaji Muttaqa Isa, ya yaba da wannan shiri tare da alkawarin goyon bayan kawar da kayayyakin jabu da tsauwala farashi a kasuwar.