Gwamnan Kano ya naɗa sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnati

0
25

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Dr. Suleiman Wali Sani, mni a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kano.

Bayanin hakan na  cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Dr. Sani, ya kasance ƙwararren likita kuma masanin tsara manufofi, kuma tsohon Babban Sakatare, ne wanda ya shafe fiye da shekaru 40 yana hidima a ma’aikatun gwamnati.

Kafin wannan sabon mukami, ya rike matsayi na Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Ma’aikata.

Haka zalika, ya jagoranci manyan asibitocin jihar kamar Asibitin Murtala Muhammad da Muhammad Abdullahi Wase.

A wani cigaban kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Manjo Janar Mohammed Sani (Rtd.), fitaccen tsohon jami’in soja wanda ya shafe fiye da shekaru 35 yana hidima a Rundunar Sojin Najeriya, a matsayin sabon Darakta Janar na Harkokin Musamman a Gidan Gwamnati.

Manjo Janar Sani ya rike mukamai da dama a matsayin kwamanda da jami’in tsare-tsare a matakai daban-daban, inda ya taka muhimmiyar rawa a sha’anin zaman lafiya, warware rikice-rikice da tsaro na ƙasa.

Gwamnan ya taya sabbin manyan jami’an murna tare da umarnin su fara aiki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here