Fitaccen ɗan siyasa kuma dattijo a harkokin ƙasa, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa bai da alaƙa da kowace jam’iyya ko ƙungiyar siyasa, yana mai cewa yanzu hankalinsa ya karkata ne kawai wajen abubuwan da za su haɓaka ci gaban Najeriya.
Yakasai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano a ranar Laraba, inda ya ce burinsa shi ne ganin Najeriya ta ci gaba, maimakon tsunduma cikin harkokin siyasa.
Ina so in jaddada cewa bana cikin kowace ƙungiyar siyasa. Abinda nake da sha’awa yanzu shi ne samar da tsare-tsare da shirye-shirye da za su kawo cigaba a ƙasarmu, in ji shi.
Jawaban Yakasai sun zo ne a daidai lokacin da ake ta samun canje-canjen siyasa da ɗaukar matsayar ƴan siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027, inda ’yan siyasa da dama ke neman goyon bayan dattawan ƙasa da fitattun ’yan Najeriya.
Sai dai Yakasai ya bayyanawa duniya cewa babu shi babu shiga harkar siyasa ta bangare ko wata jam’iyya a halin yanzu.