Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da kama mutane 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, a wani sabon samamen tsaro da ta kaddamar mai suna “Operation Kukan Kura”, wanda aka fara domin tabbatar da tsaro da yaki da miyagun laifuka a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar rundunar da ke Bompai, Kano, ranar Alhamis.
Ya ce an fara wannan aiki ne tun daga ranar 1 ga Yuli, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, domin karfafa hulɗa da al’umma wajen yaki da laifuka da kuma karfafa tsarin ‘yan sanda masu dogaro da hadin kan jama’a.
A cewar CP Bakori, an mayar da hankali musamman wajen yaki da ‘yan daba a cikin birnin Kano, masu garkuwa da mutane da ke kan iyakokin jihar, safarar miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u. Cikin kwanaki 24 da fara wannan aiki, an kama mutane 98 da ake zargi da hannu a manyan laifuka 21, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, ‘yan daba, safarar kwayoyi, satar motoci, damfara da dai sauransu.
Cikin wadanda aka kama akwai:
Masu garkuwa da mutane: 4
‘Yan fashi da makami: 21
Masu safarar miyagun kwayoyi: 5
Masu satar mota: 12
Masu damfara: 4
Barayi: 5
‘Yan daba: 47
Haka zalika, rundunar ta kwato kayayyaki da dama, ciki har da:
Motoci da aka sace: 6
Babura ƙafa uku-uku: 8
Babura: 10
Wayoyin hannu: 13
Wuka: 98
Adduna: 16
Batir din mota: 5
Haka kuma an kama miyagun kwayoyi da dama ciki har da:
Wiwi fiye da guda 1,000
Kwayoyin Exol da diazepam
Roba 86 na sinadarin “suck and die”
Dalar Amurka jabu har $10,000