Rundunar sojin musamman ta Operation Safe Haven (OPSH) ta tabbatar da mutuwar jami’an sa-kai guda takwas a wani harin kwanton-bauna da ‘yan bindiga suka kai musu a karamar hukumar Kanam, Jihar Filato, ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce jami’an vigilante ɗin sun shirya wani samame ba tare da sanar da sojoji ba, kuma sun kai hari kan fararen hula a unguwar Kukawa, inda suka kwace babura fiye da 20 tare da kwasar kaya daga shaguna.
A yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa dajin Odare, sai ‘yan bindiga suka kai musu hari, suka kashe takwas daga cikinsu, yayin da wasu suka ɓace. Sanarwar tace Sojoji na ci gaba da bincike don gano waɗanda suka ɓata bayan kaiwa yan sa kai harin.
OPSH ta gargadi ƙungiyoyin sa-kai da su daina gudanar da ayyuka ba tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro ba, domin hakan na jefa rayukan su cikin haɗari.
Kafin yanzu dai an bayyana rahoton cewa harin ƙwantan ɓauna da ƴan ta’addan suka kaiwa yan sa kai yayi sanadiyar mutuwar jami’an sa kai 70, sannan an rasa inda wasu da dama suka shiga, sai dai sanarwar sojojin ta nuna cewa adadin waɗanda aka kashe bai kai haka ba.