Wani mummunan lamari ya faru a yankin Choba da ke birnin Port Harcourt, Jihar Ribas, inda wata ɗalibar Jami’ar Port Harcourt (UNIPORT) mai juna biyu, mai suna Cynthia Chukwundah, ta kona saurayinta Sunny Amadi, mai shekara 32, har lahira.
Duk da cewa ba a tabbatar da cikakken abin da ya jawo lamarin ba, wasu maƙwabta sun shaida wa Daily Trust cewa rikicin ya fara ne daga wata ƙaramar rigima da ta barke tsakaninsu.
Rahotanni sun nuna cewa Sunny Amadi, ne ya yiwa Cynthia cikin da take ɗauke da shi.
Bayan faruwar lamarin, Cynthia ta gudu daga wurin da hakan ta faru, amma daga bisani ‘yan sanda suka kama ta. Zuwa yanzu ana kuma kula da ita a asibiti saboda raunukan wuta da ta samu a jikinta yayin da ta banka masa wutar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
Ta bayyana cewa Cynthia na samun kulawar likitoci a asibiti, kuma saboda mawuyacin halin da take ciki, har yanzu ba zata iya bayar da cikakken bayani kan abin da ya faru ba. Sai dai za a ci gaba da bincike da zarar lafiyarta ta inganta, inji sanarwar.