Matar tsohon Gwamnan Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.
Zainab, ta kasance yar asalin Nangere a Jihar Yobe, ta bayyana hakan a wani taron mata na jam’iyyar ADC da aka gudanar a Damaturu.
Ta soki gwamnatin APC karkashin Shugaba Bola Tinubu kan rashin tsaro, hauhawar farashi da rashin shugabanci na gari.
Ta ce ta yanke wannan shawara ne tare da shawarwarin tsohon Ministan ‘Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, wanda yake ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP.
Zainab ta kuma bukaci mata da matasa da su shirya tun yanzu domin tunkarar babban zaɓen 2027.