Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bukaci iyaye da su cigaba da ɗaukar nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu domin dakile matsalar satar waya da ta’addancin da matasa ke aikatawa.
Shugaban Hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar haɗin gwiwa da suka kai wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Bakori. Ya ce rashin tarbiyya daga gida da kuma gazawar al’umma ne ke haddasa karuwar laifuka.
Yace hukumar na aiki da hukumomin shari’a da tsaro don ganin an hukunta masu laifi yadda ya kamata, ciki har da tattaunawa kan cire zabin tara a matsayin hukunci ga masu satar waya.
Kwamishinan ‘yan sanda ya yaba da wannan yunƙuri, yana mai tabbatar da cewa rundunarsa za ta ci gaba da aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin inganta tsaro a jihar.