Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ƙara tsaurara sharuɗɗan samun biza ga ‘yan Najeriya, shekara guda bayan ta dage haramcin biza da ya ɗauki tsawon shekaru biyu.
Sabuwar dokar ta hana ‘yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45 samun bizar yawon buɗe ido idan zasu je ƙasar su kaɗai. Sai dai za su iya neman idan suna tare da wani.
Haka zalika, duk wanda ya haura shekaru 45 dole ne ya gabatar da bayanan asusun bankinsa na watanni shida, inda kowanne wata dole ya nuna ajiyar dala 10,000 ko daidai da hakan a Naira.
UAE ta kuma dakatar da bayar da bizar wucewa (transit visa) ga ‘yan Najeriya gaba ɗaya, abin da zai iya rage zirga-zirgar jirage daga Najeriya zuwa birnin Dubai da sauran sassan UAE.
Masana harkokin tafiye-tafiye sun nuna damuwa cewa wannan mataki na iya ƙara tsananta halin da ‘yan Najeriya ke ciki wajen samun izinin shiga ƙasar.