Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa wasu gwamnoni da manyan ‘yan jam’iyyar APC na marawa hadakar jam’iyyun adawa baya a ɓoye, domin kifar da gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.
A wata hira da aka yi da shi a talbijin ta TVC, Babachir ya ce wasu daga cikin su ba su da ƙarfin hali akan su fito fili su bayyana kansu, amma suna shaida masa goyon bayansu.
Ya ce tun da daɗewa yana adawa da jam’iyyar APC duk da cewa yana cikin ta, domin yana zargin jam’iyyar da danniya da hana ‘yancin fadar ra’ayi.
A cewarsa, a siyasance mutum na iya kasancewa cikin wata jam’iyya amma yana goyon bayan ɗan takarar wata jam’iyya daban, kamar yadda wasu ‘yan APC ke yi, yana mai cewa Wike ne jagora a wannan salon siyasa.
Babachir ya ƙara da cewa APC ba ta da haɗin kai, kuma da dama daga cikin magoya bayan Tinubu sun gaji dashi suna neman zaɓi mafi nagarta.