Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnati ta sanya shekaru 16 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da ɗalibi zai iya shiga jami’a ko wata makarantar gaba da sakandire.
Alausa ya bayyana hakan ne a lokacin gudanar da wani taro da hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire JAMB a Abuja, inda ya ce wannan matakin ya maye gurbin tsohon tsarin da ke buƙatar shekaru 18, kafin dalibi ya samu gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire.
Ministan ya ce an yanke wannan hukunci ne domin daidaita wayewar kwakwalwa da shirye-shiryen ɗalibai, tare da jan kunnen cibiyoyin ilimi da su tabbatar da bin ƙa’idar.
Ya ƙara da cewa za a bar ƙalilan daga cikin ɗaliban da ke da basira ta musamman su rubuta jarrabawa ko da ba su kai shekaru 16 ba, amma dole ne a gabatar da hujjoji da takardun da ke tabbatar da hakan.
Ya gargadi duk wanda ya yi ƙoƙarin sauya shekarun haihuwarsa domin ya shiga makaranta da wuri, yana cewa za a ɗauki matakin doka a kansa.