Ƴan jaridu na taimakawa wajen kiyaye afkuwar haɗura—FRSC

0
14

Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano FRSC, ta bayyana kudirinta na ƙarfafa haɗin gwiwa da reshen wakilan kafafen yada labarai dake cikin kungiyar ƴan jaridu ta kasa NUJ domin inganta tsaron hanya da wayar da kan jama’a.

Kwamandan hukumar, Muhammad Bature, ne ya bayyana haka yayin da yake karɓar sabon shugabancin kungiyar ƴan jaridu reshen wakilan kafafen yaɗa labarai NUJ a hedikwatar FRSC da ke Kano.

 Ya yaba da ziyarar, da ƴan kungiyar suka kai masa yana mai jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen kare rayuka a tituna.

Bature ya gayyaci ‘yan jarida su shiga aikin sa kai na Special Marshal don taimakawa yaki da haɗurran hanya.

Shugaban kungiyar, Murtala Adewale, ya ce ziyarar na nufin ƙarfafa dangantaka da tallafa wa ayyukan FRSC, tare da ba da gudunmawa wajen yaɗa shirye-shiryen wayar da kan jama’a akan kiyaye afkuwar haɗura da kare rayukan al’umma.

An ƙare taron ne da alkawarin haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu don rage haɗurra da inganta tuki mai aminci a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here