Yunwa na kashe malaman jami’o’in Najeriya—Farfesa Balarabe

0
6

Ɗaya daga cikin manyan malaman jami’o’in Najeriya, Farfesa Balarabe Abdullahi, ya bayyana cewa malaman jami’o’in Najeriya na cikin halin ƙunci da rashin wadata saboda gwamnatin tarayya bata ɗauke su da muhimmanci ba.

Farfesa Balarabe, ya kasance malami a jami’ar Ahmadu Bello, dake Zariya, wanda ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawar da ƙafar yaɗa labarai ta RFI HAUSA, tayi dashi wadda Daily News 24 Hausa, ta bibiya.

Muna iya shafe kwanaki 40, ba tare da an biya mu albashi ba, don haka dole ne mu nemi wata hanyar don samun ƙarin kuɗin da zamu biya bukatun mu dana yaran mu, inji shi.

Ya kara da cewa a lokuta da dama abokan aikin su Farfesoshi suna yin kuka akan cewa an yi kwanaki 2 zuwa 3 ba tare da an yi girki a gidajen su ba, saboda tsabar talaucin da suke ciki.

Babu wani farfesan da zai iya saka yaron sa a makarantar kuɗi in har da albashin sa ya dogara, ballantana ace ya hau mota, ya kara da cewa.

Farfesa Balarabe, yace a lokacin da aka yi yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, na watanni 8 malamai da yawa sun mutu, wasu iyalan su sun mutu, saboda babu albashi, babu kuɗin cin abinci ko zuwa asibiti.

Da aka tambaye shi me ne ya kawo hakan, cewa yayi gwamnati ce bata son gyara tsarin albashin malaman jami’a sakamakon har yanzu an gaza cika alkawarin da suka yi da gwamnatin tarayya na yarjejeniyar shekarar 2009.

Balarabe, ya koka akan cewa albashin Farfesoshi bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta dana wasu malaman kwalejin ilimi ta tarayya duk da cewa basu kai darajar Farfesoshi ba. 

Ko a yanzu haka, dai kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta tsunduma yajin aiki, sakamakon rashin biyan su albashin watan Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here