Matatar Dangote ta a sake rage farashin  litar man Fetur zuwa Naira 820

0
5
man fetur
man fetur

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga Naira 840 zuwa Naira 820 ga ƴan kasuwar dake saro man daga matatar.

Wannan saukin farashi na zuwa ne mako guda bayan matatar ta sanar da rage farashin daga Naira 880 zuwa Naira 840.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina, ya fitar a ranar Talata, ya ce sabon farashin zai fara aiki nan take.

“Mun rage farashin daga Naira 840 zuwa Naira 820 ga kowace lita, kuma hakan zai fara aiki nan da nan,” in ji Chiejina.

Ya bayyana cewa ragewar da aka yi a baya zuwa Naira 840 ta samo asali ne sakamakon hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya, musamman a lokacin rikicin kwanaki 12 da ya faru a Gabas ta Tsakiya wanda ya dagula kasuwar.

Chiejina ya kara da cewa kamfanonin da ke da haɗin gwuiwa da matatar Dangote kamar su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil, ana sa ran za su fara siyar da man a sabon farashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here