Kungiyar ASUU ta dakatar da yajin aikin data fara

0
7

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da yajin aikin data fara bayan gwamnati ta fara turawa mambobin kungiyar albashin watan Yuni na shekarar 2025.

Wannan mataki ya biyo bayan samun tabbacin cewa mambobin ƙungiyar sun fara karɓar albashinsu kafin ƙarfe goma sha biyu na dare a ranar Lahadi, 7 ga Yuli.

Shugaban reshen ASUU na Jami’ar Abuja, Dr. Sylvanus Ugoh, ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata, yana mai cewa an yanke shawarar janye yajin aiki da aka shirya yi bayan tabbatar da cewa an fara biyan albashin.

Kafin biyan albashin, kwamitin zartarwar ASUU na ƙasa ya cimma matsayar aiwatar da manufar “ba biya ba aiki”, saboda yawan jinkirin da ake samu wajen biyan albashi, wanda suka danganta da ofishin Akanta Janar na Ƙasa.

ASUU ta zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula game da jin daɗin malaman jami’a, inda suka ce jinkirin biyan albashin ba laifin tsarin biyan albashi ba ne, sai dai da gangan gwamnati ke hana fitar da kuɗaɗen.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da matsa lamba ga gwamnatin tarayya domin biyan bashin naira biliyan goma na hakkokin karin aiki da malaman, wanda har yanzu ba a biya ba duk da yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Sai dai ASUU ta yi gargadi cewa dakatarwar yajin aiki na ɗan lokaci ne, kuma za su iya komawa idan aka sake samun jinkiri ko rashin gaskiya wajen biyan hakkokinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here