JAMB ta ƙayyade mafi Ƙanƙantar makin shiga Jami’a da kwaleji

0
6

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da ɗalibai za su samu domin samun gurbin karatu a jami’o’i.

An yanke wannan hukunci ne a taron da hukumar ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, inda aka tattauna tsarin bayar da guraben karatu na shekarar 2025.

Haka kuma, JAMB ta ƙayyade maki 140 a matsayin mafi ƙanƙantar maki na shiga kwalejojin koyon aikin jinya, yayin da za a buƙaci maki 100 don shiga kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma.

Rahotanni sun nuna cewa akwai gagarumar faɗuwa a sakamakon jarabawar JAMB da aka rubuta a bana, lamarin da ke zama babban ƙalubale ga ɗalibai da iyayensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here