ASUU ta tsunduma yajin aiki saboda rashin albashi

0
6

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta fara yajin aiki a fadin ƙasa saboda rashin biyan mambobin ta albashin watan Yuni 2025.

 Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya ce matakin ya biyo bayan shawarar da aka ɗauka a yayin taron majalisar zartarwar ASUU ta ƙasa (NEC), wadda ta umarci mambobin su dakatar da aiki idan ba a biya albashi cikin kwanaki uku ba.

Ya ce tun bayan cire su daga tsarin IPPIS zuwa GIFMIS, jinkirin biyan albashi ya zama ruwan dare, kuma gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba duk da tattaunawa da suka yi da manyan hukumomi.

ASUU ta ce wannan yajin aiki ba sabon yunkuri ba ne, amma martani ne ga wahalhalun da mambobinta ke fuskanta, ciki har da bashin biliyan 10 na alawus ɗin ƙwarewar aiki (EAA) da suke bi.

 Ƙungiyar ta ce ba za ta koma aiki ba har sai an biya hakkokin malaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here