Wasu da ake zargin Yan daba ne sun shiga makarantun sakandire na Mai Kwatashi da Commercial dake unguwar sabon gari a jihar kano, inda suka sace duk wasu abubuwa masu muhimmanci da suka shafi Ƙofofi, Tagogi, da sauran su.
Tsagerun sun dauki hanyar hana gudanar da karatu a wadannan makarantu domin kuwa sun shiga cikin dare sama da su 30 inda suka ɗaiɗaita tsarin makarantun.
Guda daga cikin tsofafin daliban makarantar mai suna Bashir Sharif Ibrahim, yace lamarin ya basu mamaki yadda irin wadannan matasan suka rushe makarantar Firamare ta Zawa’i kafin shigowa wannan makarantu
Daily News 24 Hausa, ta samu zarafin zuwa hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano, akan wannan lamari inda shugaban hukumar Rabi’u Sale Gwarzo, yace sun sami labarin faruwar hakan, kuma tuni suka dauki matakin kawo masu gadi a makarantun don hana samun afkuwar haka a nan gaba.