Aƙalla mambobin ƙungiyar sa-kai 70 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu a ƙauyukan Kukawa da Bunyun da ke ƙaramar hukumar Kanam, Jihar Filato.
Shugaban sa-kai na Kukawa, Aliyu Baffa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da tawagar haɗin guiwar sa-kai daga ƙaramar hukumar Wase suka fita neman sansanonin miyagun da ke addabar yankin.
Sai dai, a yayin gudanar da wannan aikin, tawagar ta fada cikin kwanton-baunar ƴan ta’adda ba tare da sani ba. Baffa ya ce ‘yan bindigar sun buɗe musu wuta da muggan makamai, inda suka kashe fiye da mutum 70 nan take.
Ya ƙara da cewa an gudanar da jana’izar ga waɗanda suka mutu tun da yammacin ranar, amma har yanzu akwai mambobi da dama da ba a san inda suke ba, wanda hakan ke haifar da fargabar cewa ana iya samun ƙarin gawarwaki a dajin.
Lamarin ya faru a nisan kimanin kilomita ɗaya daga garin Kukawa, a lokacin da ƴan sa-kai ke kan hanyar zuwa wani sansanin ‘yan bindiga da ke cikin dajin da ake kira Madam Forest, wanda ke da iyaka da jihohin Bauchi da Taraba.
Mun binne fiye da mutum 70 a Kukawa kawai. Amma muna tsammanin ana iya gano ƙarin gawarwaki daga sassan daban-daban. ‘Yan bindigar sun fi mu ƙarfin makamai, in ji Baffa.
Wani mazaunin ƙauyen Bunyun, Musa Ibrahim, ya tabbatar da harin a yankinsu, inda ya ce ‘yan bindigar sun kashe mambobin sa-kai 10 da ke gadin ƙauyen, sannan suka kona gidaje da dama.