Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa gwamna Babagana Umara Zulum, bashi da wata niyyar ficewa daga jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyyar haɗaka.
Kakakin gwamnan Dauda Iliya, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, akan wasu rahotonni da aka fitar a kafafen sadarwa masu nuni da cewa Zulum na shirin sauya sheƙa zuwa ADC daga APC.
Kakakin yace wannan batu bashi da tushe balle makama, yana mai cewa a halin yanzu ba siyasa ce a gaban gwamnan ba, burin sa shine samar da tsaro da ayyukan cigaba ga al’ummar Borno.
Iliya, ya kuma ce babu wani dalili da zai sanya Zulum, ficewa daga APC, saboda yana da alaka mai kyau tsakanin sa da gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, sannan gwamnan yana ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar APC.
Akan haka ne ya nemi a’lumma suyi watsi da waccan jita jita, tare da rokon kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta su riƙa tantance sahihan bayanan kafin wallafa labari.