Zamu cigaba da ƙalubalantar maguɗin zaɓe a Najeriya—Atiku

0
77

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai ci gaba da ƙalubalantar maguɗin zaɓe da kuma yakar mulkin da bai cika alkawura ba a Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, bayan wata ganawa da ya yi da jiga-jigan jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin tsohon minista kuma sanata, Idris Abdullahi.

Ya ce ba za a ci gaba da zaluntar ‘yan Najeriya ba alhali ƙasar na da yalwar albarkatu, yana mai zargin rashin shugabanci nagari da haifar da halin ƙuncin da ake ciki a halin yanzu.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ƙara da cewa haɗin gwiwar shugabannin jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zai taka rawa wajen samar da sauyi na gari a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here