Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ɗauki matakai na musamman domin bunƙasa noma da samar da abinci a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban Brazil, Inacio Lula Da Silva, a taron ƙasashen Brics karo na 17.
Tinubu ya ce wasu tsare-tsaren baya sun hana cigaba a fannin noma, amma yanzu Najeriya ta fara aiwatar da manufofi na farfaɗo da tattalin arziki da noma.
Ya ce Najeriya a shirye take ta kulla haɗin gwiwa da Brazil a fannonin noma, kasuwanci, makamashi, sufurin jiragen sama da haƙar ma’adinai.
Shugaban Brazil ya tabbatar da cewa ƙasar sa za ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma da Najeriya domin ƙarfafa tattalin arziki da hulɗar diflomasiyya.