Na sauka daga muƙamin shugaban kungiyoyin ƴan kasuwar Kano—SKY

0
10

Shugaban kamfanin SKY, Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai, wanda aka fi sani da SKY, ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da riƙe mukamin Uban Ƙungiyoyin ’Yan Kasuwa na Jihar Kano ba, duk da cewa an naɗa shi a matsayin shugaban gamayyar ƙungiyoyin a makon da ya gabata.

Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, kuma mai magana da yawunsa Kamal Yakubu Ali ya rabawa manema labarai, Alhaji SKY ya ce mukamin ya yi masa nauyi, kuma bayan tunani da nazari, ya yanke shawarar sauka daga kujerar bayan kwanaki uku da naɗin.

A cewarsa, Jama’a muna ƙara godiya da duk wata ni’ima da Allah ya yi mana, da kauna da girmamawar da ake nuna mana dare da rana. Ina ba da haƙuri tare da fatan alheri ga gamayyar ƙungiyoyin ’yan kasuwar Kano bisa naɗin da suka yi min. Amma wannan matsayin ya yi min nauyi, ba zan iya ɗauka ba. Sai dai zan ci gaba da zama tare da su a duk inda ake buƙatar gudunmawata.

Alhaji SKY ya kuma mika ta’aziyya ga al’ummar Najeriya baki ɗaya bisa rasuwar fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu kwanan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here