Khameni ya fito bainar jama’a karon farko bayan yaƙin Iran da Isra’ila

0
11

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana a bainar jama’a a karo na farko tun bayan barkewar rikici tsakanin Iran da Isra’ila, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka tabbatar.

A wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Iran ya wallafa, ya nun Ayatollah Khamenei yana gaisawa da masu ibada a wani masallaci ranar Asabar, yayin wani biki na musamman kafin bikin Ashura na mabiya Shi’a.

Fitowar da ya yi a baya-bayan nan ita ce lokacin da ya gabatar da jawabi da aka ɗauka a bidiyo, a tsakiyar yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila tun ranar 13 ga watan Yuni, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliyar Iran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here