Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara aiwatar da tsarin sufuri kyauta ga ma’aikatan gwamnati, masu ritaya da kuma ɗalibai daga ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025, a ƙarƙashin shirin Kaduna Subsidised Transport Scheme (KSTS).
Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna (KADSTRA), Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an keɓe motocin haya na musamman da za su dinga ɗaukar waɗannan rukuni na mutane kyauta har na tsawon watanni shida.
A cewarsa, dukkan ɗalibai daga matakin firamare har zuwa jami’a, ko na makarantu na gwamnati ne ko masu zaman kansu, za su amfana da wannan tsari. Ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamna Uba Sani na rage wa ma’aikata, tsofaffin ma’aikata da kuma ɗalibai matsin rayuwa.
Ibrahim ya bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su nuna katin shaidar aiki da kuma lambar NIN kafin su hau motocin, domin hana amfani da tsarin ta hanyar da ba ta dace ba. Ga ɗalibai kuwa, sai sun kasance cikin kayan makaranta kafin su sami damar hawa, yayin da jami’an tsaro daga hukumomin gwamnati da aka tantance za su gabatar da shaidarsu ta aiki kafin su hau.
Ya kuma jaddada cewa za a gudanar da aikin cikin tsari da kulawa ta musamman ta fuskar tsaro da bin ƙa’ida, domin tabbatar da inganci da aminci. Ya buƙaci hadin kan al’umma da jami’an sufuri wajen tabbatar da nasarar shirin.
Motocin farko za su fara aiki ne a manyan hanyoyin da aka ware daga Litinin mai zuwa, in ji sanarwar.