Allah ya yi wa shahararren mawakin yabon Annabi (SAW), Malam Abdullahi Shehu Ɗan Gano, rasuwa.
Rahoton rasuwar tasa ya fito ne daga bakin abokinsa kuma ɗaya daga cikin fitattun mawakan yabon Manzon Allah (SAW), Bashir Dandago, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar yau.
Ɗan Gano ya rasu ne bayan da ya gamu da wani haɗari tun farkon wannan makon, wanda ya jawo masa karaya sau biyu tare da raunuka a hannunsa.