Ukraine ta kama ɗan Najeriya yana taimakawa Rasha a yaƙin da suke yi

0
14

Wani ɗan Najeriya mai suna Kehinde Oluwagbemileke, ɗan shekara 29, ya faɗa hannun mayaƙan Ukraine yayin da yake yaƙi tare da mayaƙan Rasha, yana taimaka musu a yankin Zaporizhzhia.

 Rahotanni sun ce Kehinde ya zauna a Rasha na tsawon shekaru huɗu, inda aka kama shi da laifin safarar miyagun ƙwayoyi. Maimakon ya fuskanci hukunci, ya amince da shiga rundunar sojin Rasha a matsayin haya domin rage masa hukunci.

Wata kungiyar mai suna “I Want to Live” ta ce an ɗauki dubban mutane daga ƙasashen waje irin su Kehinde don su yi yaƙi a Ukraine, amma ana yawan yaudararsu kuma ana kallon su a matsayin “ƙarin kayan aikin soji marasa amfani.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta gargadi baki da su guji shiga cikin sojin Rasha, masu yaƙi da ita, tana mai ƙarfafa su da su tuntuɓi ƙungiyoyi masu taimaka wa waɗanda ke son mika wuya.

Lamarin Kehinde na cikin jerin rahotannin da ke bayyana yadda ake amfani da bakin haure a yaƙin Ukraine, ciki har da wasu ‘yan China da aka kama a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here