Wani mutum mai suna Usman Ali ya gurfanar da amaryarsa, mai suna Maryam, a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jaba, a jihar Kano, bisa zargin ta da satar masa wayoyin hannu guda uku da darajarsu ta kai kimanin naira dubu 65,000.
A zaman kotun, Maryam ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ta baro Abuja zuwa Kano ne bayan da mijinta ya rika yi mata duka, lamarin da ya tilasta mata komawa gidan iyayenta don samun mafaka.
Baya ga hakan, Usman ya kuma shigar da ƙorafi a kan wasu mata uku da ya bayyana a matsayin kawayen Maryam, yana zarginsu da hure mata kunne da kuma sa ta fita yawon da bai dace ba.
Alkalin kotun, Ustaz Rabiu Yahaya, ya bayar da belin Maryam, sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Yuli domin cigaba da shari’a.