Matashi ya kashe mahaifinsa da sanda a jihar Bauchi

0
6

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi ɗan shekara 24 bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekaru 70, a kauyen Uzum da ke ƙaramar hukumar Giade.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa matashin ya bugawa mahaifinsa sanda a kai yayin wata takaddama da ta ɓarke tsakaninsu da misalin ƙarfe 10:30 na daren Alhamis.

Wani mazaunin kauyen ya shaida cewa sun ji hayaniya daga gidan, kafin daga bisani aka wayi gari da labarin cewa saurayin ya buge mahaifinsa, wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme.

A cewarsa, “Mun kira ‘yan sanda, suka zo suka kai dattijon Babban Asibitin Giade, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa tun kafin a karɓe shi.”

Rundunar ta ce ana cigaba da bincike, yayin da wanda ake zargi ke hannun ‘yan sanda, sannan da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here