Al’ummar unguwar Bachirawa da ke cikin birnin Kano sun nuna bajinta bayan sun kama wasu matasa biyu da ake zargin suna aikata fashi da ƙwace waya a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun tare wata mata a unguwar inda suka ƙwace mata wayarta. Sai dai kafin su tsere, mazauna yankin suka taru suka cafke su tare da kwato wayar.
Haka kuma, matasan sun kwace wasu makamai daga hannun waɗanda ake zargin, kafin daga bisani su miƙa su ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai yabawa irin hadin kan da al’umma ke bayarwa wajen yaki da aikata laifuka a jihar Kano.