Harin ƴan bindiga yayi sanadiyar mutuwar sojojin Nijar 10

0
10

Gwamnatin Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojinta 10 tare da jikkatar wasu 15 a wani hari da ’yan ta’adda suka kai a yankin Gotheye, kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso.

Ministan Tsaro, Janar Salifou Modi, ya ce dakarun sojin sun mayar da martani inda suka kashe ’yan ta’adda 41.

 Harin ya auku ne a garuruwan Bouloundjounga da Samira inda ake da babbar ma’adanar zinari a ƙasar.

A baya-bayan nan, ma’aikata takwas sun mutu a Samira bayan motarsu ta taka nakiya. Nijar na ci gaba da fama da hare-haren ’yan ta’adda musamman a yankunan da ke iyaka da Mali da Burkina Faso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here