Gwamnatin Tarayya ta shirya gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki a fannin man fetur a ranakun 23 da 24 ga watan Yuli, domin tattauna matsalolin farashi da karancin samuwar fetur a kasuwa, yayin da ‘yan kasuwar mai ke kara matsa lamba kan bukatar daidaita farashin.
Francis Ogaree, Darakta a hukumar kula da tsire-tsire da harkar sarrafa danyen mai, da kayayyakin sufuri a Hukumar Kula da albarkatun mai (NMDPRA), ne ya bayyana hakan yayin zaman wata muhawara a taron makon makamashi na Najeriya karo na 24 da aka gudanar a Abuja.
Ogaree ya bayyana cewa NMDPRA ce za ta shirya taron, wanda zai hada ‘yan kasuwa, masu tace mai, ‘yan kasuwar cikin gida da jami’an gwamnati, domin tattauna batutuwan da suka shafi tsayayyen tsarin farashi, samuwar danyen mai, da kuma hanyoyin da za a bi domin daidaita kasuwar fetur bayan cire tallafin man.
A cewarsa, akwai bukatar bude tattaunawa domin karfafa tsarin farashi bayan cire tallafin mai. Ya kara da cewa hukumar NMDPRA na sane da kalubalen da masu ruwa da tsaki ke fuskanta a fannin, kuma tana daukar matakai domin samar da tsari na dindindin da kuma karfafa jari a harkar tace mai a gida.
Yayin jawabinsa a taron, Ogaree ya ce, muna ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taronmu, inda muke fuskantar matsaloli tare da neman hanyoyin magance su.
Dangane da batun farashin mai, wanda yanzu ke kara janyo cece-kuce, Ogaree ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da aiki a kai, kuma wannan ne dalilin da ya sa za a gudanar da taron a karshen wannan wata domin maida hankali kan batun farashi.
Ya ce taron zai rage damuwa da kuma samar da tsari mai dorewa, yana mai cewa kowa ya san cewa batun farashin fetur abu ne mai sarkakiya wanda ke bambanta daga kasa zuwa kasa, kuma hukumar tana aiki tukuru domin shawo kan matsalar.
A ranar 16 ga Yuli, Kungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas (PENGASSAN) ta bayyana cewa ya kamata a rika sayar da lita ɗaya na fetur tsakanin Naira 700 zuwa Naira 750 a matakin kasuwa.