Ɗan Shekara 70 ya kashe ƙanwarsa akan rikicin Gado

0
10

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani tsoho mai shekaru 70 da haihuwa, mai Adamu Yakubu, bisa zargin kashe ƙanwarsa Hannatu Hashimu, mai shekaru 45, a sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakaninsu kan rabon gadon gona a ƙauyen Galadanchi, ƙaramar hukumar Dutse.

Kakakin rundunar, SP Lawan Shi’isu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa rikicin ya samo asali ne bayan saɓani tsakanin Adamu da ƙanwarsa game da mallakar wani ɓangare na gona da suka gada.

Bayanan farko na binciken ƴan sanda sun nuna cewa yayin da taƙaddama ta yi zafi, Adamu ya dauki sanda ya buge ƙanwar tasa, lamarin da ya janyo rikici mai tsanani tsakanin su.

Bayan afkuwar lamarin, Hannatu ta koma gidan aurenta cikin fushi, inda daga bisani ta fadi ta suma. An garzaya da ita zuwa Babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cafke wanda ake zargi, tare da ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin domin gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here