Wata kotu a Awka, Jihar Anambra, ta bada umarnin tsare wani likita mai shekaru 72, Dr. Daniel Ikebuilo, da mata biyu Ifunanya da Chidiogo Ogbonna, kan zargin satar yaro da sayar da shi.
An zargi mata biyun da dauke yaro dan shekara bakwai daga wajen mahaifiyarsa a Onitsha, sannan suka sayar da shi ga likitan a kan Naira dubu 700, wanda shi kuma ya sake sayar da yaron a kan Naira miliyan 2 da dubu É—ari 3.
Lauyar gwamnati ta bayyana cewa wadanda ake tuhuma sun taba gurfana a kotu a baya kan makamancin wannan laifi, amma bayan samun beli, suka sake aikata wani laifi makamancin haka.
Kotu ta dage sauraron bukatar belinsu zuwa 13 ga watan Agusta.