Takaddama ta ɗauki zafi tsakanin FIRS da KEDCO a jihar Kano

0
13

Wata gagarumar takaddama ta kunno kai a jihar Kano yayin da Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta kulle babban ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), saboda bashi na haraji da ake bin kamfanin da ya kai daruruwan biliyoyin naira.

Wani ma’aikacin KEDCO da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya shaida cewa tun tsawon kwanaki tara da suka gabata, an kulle babban ofishin kamfanin da ke Kano, kuma ba a bar wani ma’aikaci ya shiga ciki.

“Ina nan lokacin da jami’an FIRS suka iso ɗauke da umarnin kotu kafin su kulle ofishin. Idan ka lura da kyau, ma har masu tsaron ofishin sun tsaya a waje. Motocin sintirinmu duk suna nan a cikin harabar ofishin, kuma ba mu da damar fitar da su,” in ji ma’aikacin.

A wani mataki na mayar da martani, KEDCO ta yanke wutar lantarki daga dukkanin ofisoshin FIRS da ke fadin Kano, lamarin da ya kara jefa al’amura cikin rudani tsakanin ɓangarorin biyu.

A lokacin da akayi kokarin neman karin bayani Jami’in Hulda da Jama’a na KEDCO, Malam Sani Bala, ba’a same shi ba, sakamakon layinsa bai shiga ba.

Haka zalika daga ɓangaren FIRS ma ma’aikatan sa sun ki bayar da wata sanarwa a hukumance kan wannan dambarwa.

Sai dai wata majiya daga cikin FIRS ta bayyana cewa bashin harajin da ake bin KEDCO ya samo asali tun shekaru shida da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here