Buba Galadima, babban jigo a jam’iyyar NNPP, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar duk da matsin lamba daga wasu jam’iyyun da ke kokarin janyo shi cikin su.
Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin “The Morning Show” na Arise Television a ranar Juma’a.
A kwanakin baya, rahotanni sun yadu cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC mai mulki wani ci gaban da wasu suka danganta da murabus din Abdullahi Ganduje daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Sai dai Galadima, wanda ya dade yana tare da Kwankwaso, ya ce jam’iyyun PDP, APC da kuma wasu daga cikin hadakar siyasa sun riga sun yi ƙoƙarin jawo Kwankwaso zuwa garesu.
A cewarsa, Kwankwaso ya nuna kwazo da biyayya ta hanyar ci gaba da zama cikin NNPP duk da kiraye-kirayen da ake masa daga bangarori daban-daban.
Galadima ya bayyana Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin ɗan siyasa mai hangen nesa da dabaru, inda ya ce shirunsa ma yana ƙara masa daraja a idon jama’a.
Ya ƙara da cewa dukkan manyan jam’iyyun kasar nan sun san kimarsa a siyasa.
Galadima ya jaddada cewa duk da kiraye-kirayen da Kwankwaso ke samu daga PDP, APC da sauran kungiyoyi, har yanzu yana nan daram a NNPP cikin dabaru da shiri mai zurfi.