Kotu ta umarci majalisa ta dawo da Sanata Natasha kan muƙamin ta

0
12

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci Majalisar Dattawa da ta janye dakatarwar watanni shida da ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Mai shari’a Binta Nyako ta bayyana hukuncin dakatarwar a matsayin mai tsanani, tare da cewa ya tauye wa jama’ar mazabarta damar samun wakilci.

Kotun ta ce dokokin da majalisar ta dogara da su wajen dakatar da sanatar sun wuce gona da iri, kuma ba su fayyace iyakar lokacin da ake iya dakatar da dan majalisa ba.

Sai dai kotun ta amince cewa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, bai yi kuskure ba wajen hana Natasha magana a zauren majalisa, duba da ba ta zaune a kujerarta ta hukuma.

Kotun ta kuma yi watsi da hujjar Akpabio cewa batun harkar cikin gida ce ta majalisa, inda ta tabbatar da cewa kotu na da hurumin sauraron karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here