Gwamnan Kano yayi naɗin sabbin muƙamai

0
11

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin nade-nade muƙamai da nufin karfafa hukumomi da kuma inganta ayyukan gwamnati a fadin jihar.

Jawabin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

Jerin sabbin nade naden sun haɗar da, 

Dr. Bashir A. Muzakkar, Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Bayanai ta Jihar Kano (KASITDA), wanda Kafin wannan nadin, ya kasance mai baiwa gwamna shawara kan Tattalin Arzikin Zamani da Kirkira.

Kabiru Saidu Dakata, Shugaban Hukumar Tallace-tallace ta Jihar Kano (KASA).

Dr. Fatima Abdul Abubakar (Amneef) a matsayin shugabar Hukumar Kare Jin Dadin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), wadda Kafin nadin, ta kasance mai baiwa gwamna shawara kan Wayar da Kai da Kwadago.

Injiniya Isyaku Umar Kwa, Mataimakin Darakta na hukumar Gidaje ta Jihar Kano.

Hamisu Musa Gambo Danzaki,  shugaban Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano.

Barr. Isma’il Nasarawa, shugaban Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa.

Captain Mohd Bello Maigaskiya Gabasawa (Rtd.) – Kwamandan Cibiyar Tsaro ta jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa sabbin jami’an da aka nada za su yi amfani da kwarewarsu da jajircewarsu wajen tafiyar da manufofi da hangen nesan gwamnati zuwa babban matsayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here