Yan Majalisar wakilai 7 sun sauya sheƙa zuwa APC

0
31

Akalla ‘yan majalisar wakilai shida na jam’iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙarsu zuwa jam’iyyar APC.

Cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai, Unyime Idem, mai wakiltar mazaɓar Ukanafun/Oruk Anam, sai Esin Etim, mai wakiltar Mbo/Okobo/Oron/Udung Uko/Urue, da Ekpo Asuquo, mai wakiltar Etinan/Nsit Ibom/Nsit Ubium, da Uduak Odudoh, mai wakiltar Ikot Abasi/Mkpat Enin/Eastern Obolo, da Okpolupm Etteh, mai wakiltar Eket/Esit Eket/Ibeno/Onna, da kuma Okon Bassey, mai wakiltar Itu/Ibiono Ibom.

Shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikar sauya sheƙar ‘yan majalisar yayin zaman majalisa da aka gudanar a ranar Alhamis.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar PDP ne ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki.

Baya ga su, wani ɗan majalisa daga jam’iyyar YPP, Emmanuel Ukpong-Udo, wanda ke wakiltar mazaɓar Ikono/Ini, shi ma ya koma APC.

Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Kingsley Chinda, ya nuna rashin amincewarsa da sauya sheƙar, yana mai cewa barin jam’iyyar da ta ɗora ɗan takara a kan kujerar da ya ci zaɓe, na iya jefa demokuradiyya cikin haɗari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here