Ministan Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin fasahar zamani, Dr. Bosun Tijani, ya kaddamar da dandalin fasahar zamanin da aka lalata a jihar Kano, a wani muhimmin aikin da ake sa ran zai ƙarfafa ci gaban fasaha da samar da damarmaki a tattalin arzikin arewacin Najeriya.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a harabar wurin da aka gyara bayan lalacewar da ya samu sakamakon tarzomar da ta auku a faɗin ƙasar a ranar 1 ga Agusta, 2024, lokacin zanga-zangar yaki da gurbataccen shugabanbanci.
Kodayake an kammala aikin tun bara, wanda kamfanin IHS Towers ya taimaka wajen dawo da shi cikin yanayi mai kyau.
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron, ya gode wa Minista Tijani, bisa jajircewarsa wajen ganin an kammala aikin.
“Shigar Dr. Bosun Tijani da kamfanoni masu zaman kansu irin su IHS Towers cikin irin waɗannan ayyuka alama ce ta jajircewa da haɗin guiwar da ke samar da sakamako mai y,” inji Gwarzo.
“Wannan waje dama ce ga matasa kuma juyin juya hali ne ga tattalin arzikin fasahar zamani a arewa.”
Wakilin kamfanin IHS Towers, Kazeem Oladepo, ya ce suna da ƙudurin ci gaba da tallafa wa cigaban fasaha da samun damar intanet ga al’ummar Kano.
“Mun shirya aiki tare da gwamnatin jihar Kano domin inganta ci gaban fasaha da bai wa kowa damar shiga sahun zamani,” inji shi.
Dr. Tijani ya bayyana cewa wannan dandalin fasahar zamani muhimmin ɓangare ne na shirin gwamnatin tarayya na bunƙasa harkar fasaha a faɗin ƙasa.