Kotu ta yankewa Tsulange hukuncin shekara ɗaya a gidan yari

0
11

Kotun Majistare mai lamba 21 da ke zamanta a Gyadi-Gyadi, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke wa wani matashi mai suna Umar Hashim wanda aka fi sani da Tsulange, hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari ko kuma biyan tara ta Naira 80,000.

An yanke wannan hukunci ne bayan samunsa da laifin rashin da’a, inda aka kama shi yana wanka a bainar jama’a sanye da rigar mama a unguwar Fagge.

Baya ga tarar Naira 80,000, kotun ta kuma umurce shi da ya biya Naira 20,000 a matsayin kuɗin wahala ga Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, wadda ta shigar da shi ƙara.

Shugaban hukumar, Abba Almustapha, ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin yaki da munanan dabi’u a cikin al’umma, musamman a wuraren taruwar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here