Jam’iyyar LP ta bawa Peter Obi awanni 48 yayi murabus daga cikin ta

0
21

Sabon rikici ya sake kunno kai a cikin jam’iyyar Labour bayan da shugabancin jam’iyyar bangare Julius Abure, ya bai wa ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, wa’adin awanni 48 ya yi murabus daga jam’iyyar, sakamakon shiga sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da aka ƙaddamar a Abuja.

Jam’iyyar ta bayar da wannan wa’adi ne a ranar Alhamis, kwana guda bayan Obi ya bayyana tare da wasu fitattun shugabannin adawa a wajen ƙaddamar da sabuwar haɗaka karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Wannan haɗaka ta sabuwar jam’iyya na da nufin kalubalantar gwamnati mai ci a zaɓen shekarar 2027, kuma ta ɗauki jam’iyyar ADC a matsayin dandalinta na siyasa.

Amma sabanin tsofaffin ministoci Rotimi Amaechi da Abubakar Malami waɗanda suka fice daga jam’iyyar APC kafin shiga ADC, Peter Obi bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar Labour a hukumance ba duk da kasancewarsa cikin wannan sabon haɗin gwiwa.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Labour, Obiora Ifoh, ya fitar, jam’iyyar ta nesanta kanta daga haɗakar, inda ta siffanta ta a matsayin ƙungiyar ‘yan siyasar da suke neman mafitar kansu.

“An bai wa Peter Gregory Obi wa’adin awanni 48 da ya ajiye katin jam’iyyar sa na jam’iyyar Labour tun da ya shiga sabuwar haɗakar siyasa. Jam’iyyar Labour ba ta da hannu a cikin wannan tsari kuma ta nesanta kanta da duk wata manufa da su ke da ita,” inji sanarwar.

Ifoh ya zargi Obi da gudanar da wasu taruka da wasu ‘yan jam’iyyar a boye, yana ƙoƙarin jan su su koma sabuwar jam’iyyar tare da shi.

“Mun samu sahihan bayanai game da ganawa da dama da Peter Obi ke yi da wasu daga cikin mambobinmu a asirce, yana roƙonsu su koma sabuwar jam’iyyar da ya shiga. Wasu sun ƙi amincewa, amma duk wanda muka samu yana da hannu da shi, za mu buƙaci ya ajiye muƙaminsa,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here