Buhari na cigaba da murmurewa daga rashin lafiyar sa a Burtaniya—Garba Shehu

0
7

Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana karɓar magani a ƙasar Birtaniya, amma ya ce yana samun sauƙi.

Garba Shehu ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyi dangane da yanayin lafiyar Buhari, sakamakon jita-jitar da ke yawo kan halin da yake ciki.Gaskiya ne, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya jin daɗi.

Yana karɓar magani ne a ƙasar Birtaniya,” inji Shehu.Ya ƙara da cewa Buhari ya fara tafiya ne domin duba lafiyarsa na shekara-shekara, amma daga bisani sai ya kamu da rashin lafiya a can.

“Za ku tuna cewa ya bayyana cewa zai tafi ne don duba lafiyarsa na shekara-shekara. A can ne kuma ya kamu da rashin lafiya, amma ina farin cikin sanar da ku cewa yanzu yana samun sauƙi a yayin da yake karɓar kulawar ta likitoci,” inji Shehu.

“Muna yi masa addu’ar samun sauƙi da ƙoshin lafiya,” Shehu ya ƙara da haka.

Idan za’a iya tunawa tun lokacin da yake mulki, Buhari ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa birnin Landan domin kula da lafiyarsa. A shekarar 2017, ya kwashe sama da kwanaki 100 a Birtaniya yana karɓar magani kan wata cuta da ba a bayyana ba. Wadannan tafiye-tafiyen sun tsaya na ɗan lokaci yayin da annobar COVID-19, ta barke a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here