Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Liverpool da tawagar ƙasa ta Portugal, Diogo Jota, ya rasu yana da shekaru 28 bayan wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ƙasar Spain.
Hatsarin da ya yi sanadin mutuwarsa ya faru ne a babbar hanyar A-52, a kilomita na 65, kusa da garin Palacios de Sanabria da ke lardin Zamora, a arewacin Spain.
An haifi Jota a shekarar 1996, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasa da Liverpool da Portugal ke dogaro da su.
Labarin rasuwarsa ta bazata ya girgiza duniyar masu sha’awar kwallon kafa.
Jaridar wasanni ta ƙasar Spain, MARCA, ce ta ruwaito wannan lamari a ranar Alhamis, inda ta tabbatar da cewa Jota ya rasu a wurin da hatsarin ya faru.