Mai bawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin waɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya soki sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da aka ƙirƙira, yana mai cewa haɗakar ba komai ba ce illa ƙungiyar da aka kafa don ƙiyayya ga shugaban ƙasa.
Sabuwar haɗakar, wadda ta haɗa manyan ’yan siyasa da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, ta amince da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandamalin siyasar ta don shiga zaɓen 2027.
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, Onanuga ya ce haɗakar na ƙunshe da ’yan siyasa da ba su da tasiri a halin yanzu ko kuma waɗanda sun jima da janyewa daga jam’iyyar APC mai mulki.
“Wasu daga cikin mutanen da suka kwace ADC, waɗanda ake cewa ‘yan APC ne, sun bar jam’iyyar APC tun shekaru ko watanni da suka wuce,” in ji shi. “Ya kamata jama’a su guji yaudarar da ‘yan adawa ke ƙoƙarin yi ta hanyar nuna cewar suna da muhimmanci ko cewa fitar su daga APC wata illa ce.”
Onanuga ya kawo wasu sunaye domin ƙarfafa hujjarsa. “Rotimi Amaechi ya daina goyon bayan APC tun shekarar 2022 bayan da ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a hannun Tinubu. Abubakar Malami, tsohon Antoni Janar, ya nesanta kansa daga APC tun bayan da Tinubu ya karɓi mulki da kuma bayan da ya fadi a ƙoƙarinsa na zama gwamnan Kebbi. Hadi Sirika, wanda yanzu ke tare da ADC, yana fuskantar shari’a kan raba kwangila da wasu zarge-zarge. Rauf Aregbesola kuma ya aikata cin amanar jam’iyya a zaɓen Osun na baya, har ta kai ga an kore shi daga jam’iyyar bisa rashin cancanta.”
Har wa yau, Onanuga ya zargi Kashim Imam da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Chief John Odigie Oyegun, da barin jam’iyyar tun da dadewa.
“Kashim Imam ya janye daga APC tun bayan da ya gaza samun tikitin mataimakin shugaban ƙasa a 2022. Chief Oyegun kuma, wanda tsohon shugaban jam’iyya ne, ya daina sha’awar APC tun da dadewa, kuma yana cikin waɗanda suka assasa wannan haɗakar tun farko,” in ji Onanuga.
Ya bayyana haɗakar a matsayin siyasa da bata da alkibla ko manufa.”
“Shawarata ga ‘yan Najeriya, ku buɗe idonku sosai, Jam’iyyar siyasar haɗakar da ba ta da tsayayyen tsari ko akida, kuma abin daya haɗa mambobinta kawai shi ne ƙiyayya ga Shugaba Tinubu, wanda ba za ta kawo alheri ba, sai dai ta mayar da ƙasar baya.
A ƙarshe, Onanuga ya zargi mambobin haɗakar da neman mulki da nufin biyan bukatunsu, ba don al’ummar Najeriya ba.