Trump: Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza

0
25

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Isra’ila ta amince da wasu sharuɗɗa da za su taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 a Zirin Gaza.

A wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce yana fatan kungiyar Hamas za ta karɓi wannan yarjejeniya. Ya ƙara da cewa idan hakan bai samu ba, akwai yiwuwar lamarin ya ƙara tsananta maimakon samun sauƙi.

BBC ta ruwaito cewa wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da wata ganawa tsakanin Trump da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Litinin mai zuwa. A cewar Trump, zai tsaya tsayin daka wajen ganin an warware wannan rikici.

A baya dai an samu wani yunkurin tsagaita wuta, amma ya rushe a watan Maris, bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tare da ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here