PDP zata hukunta mambobin ta masu shirin komawa jam’iyyar haɗaka karkashin ADC

0
12

Babbar jam’iyyar hamayya PDP, ta fitar da gargaɗi ga mambobinta da ke ƙoƙarin shiga cikin sabuwar haɗakar siyasa da jam’iyyar ADC ke jagoranta.

Shugaban riƙon jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja, bayan kammala taron kwamitin amintattu na jam’iyyar.

Ambasada Damagum ya ce PDP ba za ta lamunci duk wani yunƙuri daga mambobinta na shiga sabuwar haɗakar ba, inda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi.

“A bayyane muke cewa babu wata jam’iyya da ta fi PDP cancanta wajen jagorantar adawa da gwamnatin APC. Amma in akwai waɗanda ke ganin za su iya yin hakan a wata hanya daban, to su gwada su gani. Dole dai su dawo,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai wasu daga cikin mambobin PDP da ke ƙoƙarin “sayar da jam’iyyar” ta hanyar shiga haɗakar, yana mai cewa hakan ba zai amfanesu ba.

Rahotanni na nuna cewa wasu jiga-jigan PDP, ciki har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, sun bayyana cikin sabuwar haɗakar ADC.

A makon nan ne jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa, inda ta bayyana cewa ta cimma matsaya wajen warware rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna addabar jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here