NAFDAC ta bayyana kalar man ƙara hasken fata mai hatsari ga lafiyar al’umma

0
31

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ja hankalin masu amfani da man shafe-shafe masu sa fata yin fari da su guji amfani da samfuran da ke dauke da sinadarin hydroquinone fiye da kima domin kare lafiyar su.

Shugaban hukumar NAFDAC na Jihar Bauchi, Hamis Yahaya, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Bauchi, ranar Talata.

Hydroquinone sinadari ne da ake amfani da shi wajen rage duhun fata ko tabon.

A cewar Yahaya, hukumar ta NAFDAC ta amince da kaso biyu kacal (2%) na hydroquinone a cikin kayan kwalliya don kiyaye lafiyar masu amfani da irin wadannan mayukan.

Ya bayyana cewa NAFDAC na gudanar da bincike a kasuwanni don tabbatar da cewa kayayyakin da ake amfani da su ba sa cutar da lafiyar jama’a.

“Fatar mutum mai duhu tana da kariya daga hasken rana saboda sinadarin melanin da ke cikinta. Amfani da man da ke dauke da hydroquinone fiye da kashi biyu cikin dari (2%) yana da illa ga lafiya. Haka kuma, hada man shafe-shafe ba tare da kwarewa ba babban kuskure ne. Hydroquinone na iya haifar da cututtuka daban-daban da suka hada da ciwon daji (cancer),” in ji shi.

Yahaya ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan illolin amfani da irin wadannan kayayyaki domin kare rayuwar masu amfani da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here