Matashi ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar doka mata Bulon ƙasa

0
12

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan wani matashi dan shekara 30 da ake zargi da kashe mahaifiyarsa mai shekara 75, ta hanyar doka mata bulon kasa a kai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Dantanoma da ke karamar hukumar Gumel a jihar. A cewar sa, an samu rahoton cewa rikici ya barke tsakanin matashin da mahaifiyarsa, inda nan da nan jami’an tsaro suka garzaya zuwa gidan. Sai dai a lokacin da suka isa, sun tarar da dattijuwar kwance cikin jini.

Yanzu haka, wanda ake zargin yana tsare a sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun karuwar rikice-rikice tsakanin iyaye da ‘ya’yansu a wasu sassan jihar. A watan Mayu na wannan shekarar ma, an kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifinsa da adda a garin Sara, karamar hukumar Gwaram.

Rundunar ‘yan sanda ta bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai wajen kai rahoton duk wani abu da ke da alamun barazana ga zaman lafiya da rayuwar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here