INEC Za Ta Bayyana Ka’idojin Duba Sakamakon Zaɓe Kafin 2027

0
33

A shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa tana ƙoƙarin fitar da ƙarin ƙa’idoji da za su jagoranci yadda za a duba sakamakon zaɓe da aka bayyana.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya sanar da hakan a taron da aka gudanar tare da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a birnin Abuja.

Farfesa Yakubu ya jaddada muhimmancin Kwamishinonin Jihohi su yi aikinsu bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa, inda ya nuna damuwa kan yadda ake fassara Sashe na 65 na Dokar Zaɓe ta 2022 wacce ta bawa INEC damar sake duba sakamakon zaɓe.

Ya ce hukumar tana aiki kan sabbin ƙa’idoji da za su fayyace hanyoyin da za a bi wajen dubawa da tantance sakamakon zaɓe.

Wannan sabbin ƙa’idoji za su kasance ƙari ne akan waɗanda ke cikin dokokin zaɓe na 2022, kuma za a wallafa su a shafin INEC nan ba da jimawa ba,” in ji Farfesa Yakubu.

Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa tuni hukumar ta gana da shugabannin jam’iyyu, ƙungiyoyin fararen hula, ‘yan jarida da jami’an tsaro domin samun haɗin kai da fahimta kafin zaɓe.

A ƙarshe, ya bayyana cewa yanzu haka dukkan jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun samu sabbin Kwamishinonin Zaɓe (RECs) da ke da cikakken iko na gudanar da ayyukan hukumar a jihohinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here